Labarai
Tsaro : Matawalle ya ce babu wani zabi da ya ragi illa yin sulhu da ‘yan binidga
Gwamnan jihar Zamfara Muhammad Matawalle na jihar Zamfara ya ce babu wani zabi da ya ragi illa a yi sulhu tsakanin gwamnati da ‘yan bindiga.
Muhammad Matawalle ya bayyana hakan ne a lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai a jihar Adamawa a yau Alhamis.
Gwamnan na Zamfara yaje jihar Adamawa ne ya yin ziyarar aiki da kuma kaddamar da wasu titina da gwamnatin jihar ta Adamawa ta aiwatar a kauyuka wanda shi ne karo na 2 a karamar hukumar Kuva-Gaya.
Matawalle ya kara da cewar, ”Ya nanata cewa hanya mafi dacewa wajen shawo kan matsalar tsaro shi ne yin sulhu da ‘yan bindiga”
Masu fashin baki kan al’amuran yau da kullum na yi wa kalaman gwamnan jihar Zamfara kallo da yin martani ga gwamnan jihar Zamfara Malam Nasir Ahmad el-Rufai na jihar Kaduna da ya ce babu hadin kai tsakanin gwamnoni wajen yaki da ‘yan bindiga a kasar nan.
You must be logged in to post a comment Login