ilimi
Tsaro: Muna ci gaba da kwashe ɗaliban mu daga Jos – El-rufa’i
Gwamnatin jihar Kaduna ta ce, ta fara kwaso ɗalibai ƴan asalin jihar da ke karatu a jami’ar Jos da sauran kwalejojin ta zuwa gida.
Shugaban hukumar bada tallafin karatu a jihar Malam Hassan Rilwan ne ya bayyana hakan a Alhamis ɗin nan, ta cikin wata sanarwa da ya fitar.
Ya ce, kwaso ɗaliban ya biyo bayan yadda jihar ke ci gaba da fuskantar matsalaolin tsaro a kwanakin nan, wanda kuma tuni gwamnatin jihar ta bada umarnin a fara kwaso su zuwa gida.
Malam Hassan Rilwan ya kuma ce, tun a ranar Juma’ar da ta gabata ne aka fara jigilar ɗaliban daga Jos zuwa jihar Kaduna, kuma za a kammala aikin a ƙarshen makon da muke ciki.
You must be logged in to post a comment Login