Labarai
Gwamnan Filato ya buƙaci a haɗa hannu don magance ayyukan ta’addanci

Gwamnan Jihar Plateau, Caleb Mutfwang, ya yi kira ga dukkan hukumomin tsaro, shugabannin al’umma da sauran masu ruwa da tsaki da su haɗa kai domin fuskantar matsalar ta’addanci da sauran ƙalubalen tsaro da ke barazana ga zaman lafiya da haɗin kan ƙasa.
Gwamnan ya bayyana cewa nasarar yaƙi da matsalolin tsaro ba za ta samu ba sai an samar da cikakkiyar haɗin gwiwa tsakanin gwamnati, hukumomin tsaro da al’umma, yana mai jaddada cewa tsaro nauyi ne da ya rataya a wuyan kowa.
Ya ce lokaci ya yi da za a ƙarfafa musayar bayanan sirri, haɗa kai wajen tattara bayanai da kuma ɗaukar matakan gaggawa domin dakile ayyukan ’yan ta’adda da masu tayar da zaune tsaye kafin su kai ga cimma mugayen manufofinsu.
You must be logged in to post a comment Login