Kiwon Lafiya
Tsohon gwamna Kano Rabiu Kwankwaso ya kai wa gwamnan jihar Ekiti ziyara
Tsohon gwamnan jihar Kano Rabi’u Musa Kwankwaso ya kai wa gwamnan jihar Ekiti Ayodele Fayose ziyarar bangirma, inda ya bukaci da a gudanar da zabe na gaskiya da adalci a zaben gwamnan jihar da za a gudanar a ranar 14 ga watan Yuli.
Rabi’u Musa Kwankwaso ya kuma koka kan yadda gwamnatin tarayya ta kasa shawo kan kashe kashen da ke faruwa a jihar Filato da wasu sassan kasar nan.
Rabi’u Kwankwaso wada mamba ne a cikin kungiyar yan sabuwar PDP da suka koma APC ya kai ziyara jihar ne domin ganawa da al’ummar Hausa Fulani da ke jihar ta Ekiti domin yin kira a gare su da su zauna lafiya da wadanda suke tare da su.
A baya bayan nan dai rahotannin sun yi nuni da cewa Rabi’u Musa Kwankwaso bai halarci babban taron jam’iyyar APC ba da ya gudana a yan kwanakin nan sakamakon bambancin fahimta.
Koda aka tambayi Kwankwaso ko yana da niyyar komawa jam’iyyar PDP ne sai ya ce matakin sa na gaba ya ta’allaka ne da matakin da kungiyar su ta Sababbin yan PDP a jam’iyyar ta APC suka yanke.
Da ya ke maida na sa jawabin gwamnan jihar ta Ekiti Ayodele Fayose ya godewa sanatan inda ya ce zaman lafiya na da matukar muhimmanci ga cigaban kowacce kasa, inda shima ya zargi gwamnatin tarayya da kasa wanzar da zaman lafiya.