Kiwon Lafiya
Tsohon gwamnan bankin CBN ya ce kamata yayi a samar da asusun tallafawa kananan masana’antu
Tsohon gwamnan babban bankin kasa CBN Farfesa Kingsley Moghalu ya bayyana cewa kamata yayi a samar da wani asusu da zai tara kudade da yawan su ya kai biliyan 500 don habaka kanana da matsakaitan masana’antu da nufin bunkasa tattalin arzikin kasar nan.
Kingsley Moghalu wanda shugaban kungiya ce mai rajin samar da ingantaccen shugabanci da tattalin arziki, ya ce samar da asusun wanda za’a rika tara kudaden ne ta hanyar kamfanoni masu zaman kansu zai taimaka wajen habaka kanana da matsakaitan masana’antu tare da ciyar da tattalin arzikin kasar nan gaba.
Farfesa Kingsley ya bayyana hakan ne a yayin wata tattaunawa da Freedom Radio, inda ya kuma ce kasashe da dama sun habaka tattalin arzikin su ta hanyar samar da makamancin wannan asusu.
Ya kuma danganta matsalolin da kanana da matsakaitan masana’antu a Najeriya ke fuskanta da rashin isassun kudaden tafiyar da su da kuma karancin ilimin tafiyar da su.
Har-ila-yau ya kuma ce naira Biliyan Biyar da gwamnati ta ware wa bangaren tare kuma da naira dubu biyar da aka alkawarta baiwa matasan kasar nan cikin wannan kudi, ba zai samar da wani sauyin da ake bukata ba, domin kuwa yawan kudin bai kai mizanin yadda zai yaki talauci cikin al’umma ba