Kiwon Lafiya
Tsohon shugaban jami’ar nazarin aikin gona ta Michael Okpara ya koka da irin farfesoshin da kasar nan ke dasu
Tsohon shugaban jami’ar nazarin aikin gona ta Michael Okpara da ke Umudike jihar Abia, farfesa Ikenna Onyido, ya koka dangane da irin Farfesoshi da jami’oin kasar nan suke yayewa wadanda ya bayyana su a matsayin malalata.
Ya kuma nuna damuwarsa kan yadda ake baiwa wadanda basu cancanta ba takardar kammala digirin digirgir, wanda ya ce hatsarinsu ya fi na Boko Haram.
Farfesa Ikenna Onyido ya bayyana hakan ne yayin da yake gabatar da mukala a wajen wani taro a jami’ar Nnamdi Azikiwe da ke Awkan jihar Anambra.
Ya ce akwai damuwa matuka kan yadda jami’oin kasar nan a wannan lokaci, su ka zamo wasu fage na yaye Farfesoshi da masu digirin digirgir wadanda kokadan basu cancanta ba.
Fitaccen malamin ya kuma ce rashin ingancin malaman jami’oin, ya taka rawa wajen gurbata halayen dalibai da ke karatu a jami’oin kasar nan, wanda ya bukaci masu ruwa da tsaki da su kawo daukin gaggawa kafin lamarin ya kai lokacin da zai gagari Kundila.