Labaran Wasanni
UCL: Real Madrid ta cire PSG
Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid tayi nasarar doke PSG da ci 3-1 a wasan da suka fafata gasar cin kofin zakarun turai Champions League.
Wasan dai ya gudana a kata faren filin wasa na Santiago Bernabo da ke kasar Spain a ranar Laraba 09 ga Maris din 2021.
Dan wasa Klyan Mbappe ne ya fara zura kwallon farko a minti na 38.
Kana bayan dawowa daga hutun rabin lokaci Karim Benzema ya zura kwallaye uku a minti na (60′)
fa 75 da kuma 77, hakn da ya bawa Real Madrid nasara a wasan.
Tin da fari a wasan farko da suka fafata a makonni biyu baya da ya gabata PSG ta doke Real Madrid da ci 1-0.
Sai dai a karawar da ta gudana a ranar Laraba, jumulla an tashi Real Madrid tayi nasara da ci 3-2 a wasa gida da waje.
Wasan dai shi ne zagaye na kungiyoyi 16, Wanda kawo yanzu Real Madrid tayi nasara kaiwa zagaye na dab dana kusa da karshe wato Quarter Final.
Real Madrid itace kungiya daya tilo da ta fi ko wacce kungiya lashe gasar da jumulla 13 a tarihi.
Wanda ta lashe gasar ta karshe a kakar wasannin shekarar 2017/2018 bayan doke Juventus a wasan karshe.
Yayinda ita Kuma PSG ke yunkurin lashe gasar a karo na farko a tarihi, bayan da a wasan karshe tayi rashin nasara a hannun Bayern Munich a shekarun da suka gabata a wasan na karshe.
A daya wasan da ya gudana a Manchester City da Sporting CP sun tashi wasa daya da daya, inda jumulla City tayi nasara gida da waje da ci 5-0.
You must be logged in to post a comment Login