Labaran Wasanni
UEFA ta janye dokar hana magoya baya zuwa wata kasar kallon wasa
Hukumar kwallon kafar Turai UEFA ta janye dokar hana magoya baya zuwa wata kasar kallon wasanni.
Dokar da za ta fara aiki a mako mai zuwa, amma bisa ga la’akari da dokar kasa da kasa ta hana yada cutar COVID-19.
Hakan na nufin ‘yan kallo daga wata kasar za su iya halartar wasannin gasar zakarun nahiyar turai ta Champions League da Europa League da kuma Europa Conference League.
UEFA: Yin gasar cin kofin Duniya duk bayan shekaru 2 zai rage karsashin ta
Sauyin dokar zai shafi kungiyoyin kasashen Ingila da Scotland, wadanda ke shirin zuwa waje buga gasar zakarun Turai cikin rukunin da za a fara daga ranar 14 ga watan Satumban shekarar 2021.
Tun bayan da aka samu bullar cutar korona ne dai aka hana ‘yan kallo daga wajen wata kasar a turai su je wata kasar kallon wasa.
Sai dai kuma an bar tsirarun ‘yan kallo a fafatawar karshe na gasar zakarun Turai ta Champions League data gudana tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Chelsea da Manchester City cikin watan Mayun shekarar 2021.
You must be logged in to post a comment Login