Labaran Wasanni
US Open 2020: Dominic Thiem ya lashe gasar tare da kafa tarihi
Dan wasa Dominic Thiem, ya samu nasarar lashe gasar kwallon Tennis ta US Open wadda aka karkare a filin wasa na Arthur Ashe Stadium dake birnin New York din kasar Amurka.
Dominic Thiem, dan kasar Austria, ya doke Alexander Zverev dan kasar Jamus da ci 2-6 da 4-6 da 6-4 da 6-3 da kuma 7-6.
Wasan wanda a ka fafata a ranar Lahadin da ta gabata, an dai shafe tsawon sama da sa’a 4 a zagaye na 5 a na fafatawa tsakanin ‘yan wasan biyu, a wasan karshe a gasar.
Zverev ya lallasa Thiem a zagaye na farko da na biyu kafin daga bisani Thiem ya lashe gasar a zagaye na uku da na hudu da kuma na biyar, yayin da hakan ya kasance shi ne karo na farko a tarihin gasar ta US Open da wannan abun ya faru.
Wannan dai shi ne karo na farko da Dominic Thiem ya samu damar daga kambun gasar kwallon Tennis ta Grand Slam a tarihin wasan sa.
You must be logged in to post a comment Login