Labarai
Uwa da yayanta 3 sun rasu sakamakon gini da ya fado musu a Zaria

Wani ginin ƙasa ya rushe ya hallaka wata uwa mai yara uku, Malama Habiba Nuhu da ‘ya’yanta biyu tare da jikarta yayin da suke barci da safiyar Laraba a birnin Zaria, karamar hukumar Zaria ta Jihar Kaduna.
Wani ganau, Mallam Ahmed wanda ke daga cikin dangin marigayiyar ya shaida wa cewa lamarin ya faru ne tsakanin karfe 3:30 zuwa 4:00 na safiyar Laraba, lokacin da katangar gida na makwabta ya rushe ya fado kansu (marasa sa’a) inda suka rasu nan take.
Mallam Ibrahim ya bayyana sunayen yaran da jikarta da suka rasu da cewa: Hauwa’u Nuhu, Aina’u Nuhu da Za’uma Nuhu. Ana cewa mahaifinsu, Mallam Nuhu Dogara, an sallame shi daga asibiti inda aka garzaya da shi domin samun kulawar gaggawa kafin a gudanar da sallar jana’izar marasa sa’ar.
Ya danganta faruwar lamarin da yanayin lalacewar katangar gidan makwabtan da ba a kula da ita ba tsawon lokaci.
Sai dai wakilinmu Hassan Ibrahim ya ruwaito cewa an binne mamatan kamar yadda addinin Musulunci ya tanada a birnin Zaria ranar Laraba.
You must be logged in to post a comment Login