Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Waɗanda suka yi rajistar APC a Kano sun ninka waɗanda suka zaɓi Gwamna Ganduje a 2019

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ce, zuwa yanzu kimanin mutane miliyan biyu da rabi ne suka yi rijistar jam’iyyar APC a Kano.

Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi yayin taro da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a fadar gwamnati.

Ta cikin wata sanarwar bayan taro da babban sakataren yaɗa labaran Gwamnan Malam Abba Anwar ya fitar, ya ce, aƙalla jam’iyyar na da mutane miliyan uku zuwa miliyan huɗu a Kano.

labarai masu alaka:

Mun fitar da jadawalin karshe na zaben cike gurbi – INEC

Hukumar zaɓen Kano ta soki tsarin yin zaɓe ta na’ura

Tun a farkon watan Fabrairu ne, jam’iyyar APC ta fara sabinta rajistar mambobinta a faɗin ƙasar nan.

Wannan adadi na miliyan biyu da rabi da Gwamnatin Kano ta bayar, na nuna cewa, yawan waɗanda suka yi rajistar jam’iyyar cikin wata guda da ƴan kwanaki ya ninka waɗanda suka zaɓi Gwamna Ganduje a zaɓen shekarar 2019.

Sakamakon zaɓen Gwamnan Kano na shekarar 2019 da hukumar zaɓe ta ƙasa INEC ta fitar ya ce, Gwamna Ganduje ya lashe zaɓe da ƙuri’u 1,033,695.

Ku latsa nan domin ganin sakamakon zaɓen na shekarar 2019

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!