Labarai
Wa zai gaji Ganduje
Tun bayan da aka fara kada gangar siyasar tunkarar babban zaben badi a Najeriya, tuni masu neman takara suka fara bayyana aniyar su ta tsayawa takara domin ɗarewa kan kujerar gwamna a Kano.
Wannan dai na nuni da cewa ko wannensu na hanƙoron ganin ya gaji gwamna mai ci a yanzu wato Dakta Abdullahi Umar Ganduje.
Kuma bayyana bukatar ta su ta neman tsayawa takara ta ƙara zaburar da wasu ƴan siyarar wajen ganin sun fito da ta su manufar.
A gefe guda kuma wasu ƴan siyasar na ci gaba kokarin sauya sheƙa daga wadda ta ba su damar ɗare wa kan madafun iko a cikinta zuwa wadda za su sake neman takara a ciki.
Zuwa yanzu dai ba a kai ga kammala sanin adadin masu muradin ɗarewa kan kujerar gwamna a zaɓen 2023 ba.
Sai dai ga wasu daga cikin waɗanda suka bayyana manufarsu kamar haka.
Abdussalam Abdulkarim A.A. Zaura
Alhaji Usman Alhaji
Sanata Barau I. Jibril
Murtala Sule Garo
Kabiru Alhassan Rurum
Alhaji Inuwa Waya
Malam Ibrahim Khalil
Sha’aban Ibrahim Sharaɗa
Muhyi Magaji Rimin Gado
Nasiru Yusuf Gawuna
Abba Kabir Yusuf
Dr Yunusa Adamu Dangwani
Ibrahim Al’ameen Little
Abin jira a gani dai ne shi ne ko wane ne zai samu nasarar ɗarewa kan karagar kujerar gwamnan Kano a 2023.
You must be logged in to post a comment Login