Labarai
WAEC ta fitar da sakamakon jarrabawar bana
Hukumar shirya jarrabawar kammala sakandare ta Afirka ta yamma WAEC ta fitar da sakamakon jarrabawar dalibai dubu casa’in da daya da dari biyu da ashirin da biyar na wadanda suka rubuta jarrabawar masu zaman kansu na bana a Najeriya.
Babban jami’in hukumar a Najeriya Mr Olu Adenipekun ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar yau, inda ya ce akalla dalibai dubu casa’in da bakwai da tamanin ne suka yi rajistar jarrabawar inda kuma dubu casa’in da hudu da da dari takwas da tamanin da hudu ne suka zauna jarrabawar a kasar nan.
Ya kuma kara da cewa akwai sakamakon jarrabawar dalibai dubu uku da dari shida da hamsin da tara da har yanzu ba a fitar da sakamakonsu ba sakamakon ci gaba da duba jarrabawar da ake yi.
Jami’ar Bayero ta kama dalibai shida da zargin magudin jarrabawa.
BUK ta kori dalibai 63 saboda satar jarrabawa
Hukumar JAMB ta sanar da ranar sake rubuta jarrabawar ga dalibai fiye 12,000
Haka zalika Adenipekun ya bayyana cewa a Najeriya dalibai dubu arba’in da bakwai da dari biyu da talatin da bakwai ne maza yayin da mata suka kasance guda dubu raba’in da bakwai da dari shida da arba’in da bakwai suka zauna rubuta jarrabawar a bana.