Kiwon Lafiya
Wakilai da masu sa idanu 700 ne ake sa ran zasu hallarci taron gamayyar Kungiyar kwadago ta kasa
Ana kyautata zaton cewa, fiye da wakilai da masu sanya idanu dari 700 ne za su halacci babban taron gamayyar kungiyar kwadago ta kasa NCL na yini 2 a babban birnin Tarayya Abuja da za’a fara yau Talata
Baban sakataren kungiyar na kasa Ozo-Eson ya shedawa manema labarai cewa taron zai maida hankali ne manyan batutuwa na kasa da kuma hadin kai a cikin kungiyar ta NLC.
Taken taron na bana shi ne, ‘’A yayin da aka kwashe fiye da shekaru ana gwagwarmaya wajen daukaka tare samar da hadin kai a tsakanin gamayyar kungiyar NLC, sake farfado da ita don bunkasa kasar nan’’ Ozo-Eson ya ce kundin tsarin daya kafa kungiyar, ya tanadi yadda za’ayi zaben wakilan kungiyar, kuma yayin taron ana kyautata zaton cewa fiye da wakilai dari 700 da suka hada da hadaddiyar kungiyar ‘yan kasuwa da ta masana’atu da dai sauran su