Labaran Kano
Wani dan daba ya tsiyaye idon wani mutum
Wani mutum mai kimanın shekaru 40 malam Salisu Yahaya ya rasa idanunsa a hannun wani dan daba mai suna Mario dake unguwar Kwalwa a karamar hukumar birni da kewaye bayan ya daba masa wuka a kwayar idonsa da wasu sassan fuskarsa.
Wannan al’amari dai ya faru ne a ranar litinin bayan malam Yahaya ya kai ziyara gun mahaifiyarsa a unguwar ta Kwalwa ,a yayin da wata hatsaniya ta shiga tsakaninsa da Mario a hanyarsa ta komawa gida.
Rahotanni sun nuna cewa Mario yana daga cikin wadanda aka sako daga gidan marin da gwamnatin Kano ta rufe a kwanakin baya.
Da yake Magana da ”yan jarida Mal Yahaya ya ce lokacin da ya baro gidan mahaifiyarsa ne ya hadu da Mario a gefen titi ya kuma bukaci da ya bashi hanya ya wuce inda Mario ya ki amince ya bashi hanyar.
Ya ce bayan ‘yar hatsaniyar da ta shiga tsakaninsu kawai sai Mario ya fito da wata wuka daga cikin aljihunsa ya kuma caka masa a idanu da wasu sassan fuskarsa.
Kafin hakan ta faru dai malam Yahaya ya ce “a lokacin da na zo wucewa ne dai nayi tuntube da kafar Mario na kuma tambaye shi dalilin da ya sa ya sanya kafarsa a kan hanya , kawai sai gani nayi jini na tsiyaya daga idanuna, tuni kuwa idona ya tsiyaye”.
Malam Yahaya ya kara da cewa Mario makwabcinsa ne domin kuwa shi a Makwarari yake yayin da su kuma suke a Kwalwa,tare da cewar bai san da me yayi amfani ba ko da wukar ne ko da wani abun na daban, kawai ya tsinci kansa cikin azaba, a don haka ne ma na nemi tallafin wani yaro da ya raka ni asibiti inji Yahaya.
Lokacin da al’amarin ya faru mutane da dama sun ga abinda ya faru wanda su ne suka yi saurin kame Mario tare da mika shi ga yan sandan Jakara , amma an zargi DPO da sallamar Mario mai tsiyaye ido.
Da muka tuntubi kakakin rundunar yan sandan jihar Kano Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce kamata yayi Yahaya ya shigar da kara na tuhumar DPO Jakara na zarginsa da sakin Mario.
Kakakin rundunar yan sanda ya ce da zarar ya shigar da kara ”Yan sanda zasu gudanar da bincike domin sanin sahihancin abinda ya faru tsakaninsa da Mario