Manyan Labarai
Wani magidanci me mata hudu yayi yaji sakamakon cin zarafi da matansa ke yi
A yayinda a ke bikin ranar cin zarafin mata ta Duniya, wani magidanci ya bayyana yadda matan sa ke cin zarafinsa.
A yanzu haka wannan magidanci me suna Malam Rabi’u dake wannan ikirari ya bayyana yadda matan sa su hudu ke cin zara finsa.
Yace yayi yaji ne tun daga garin Katsina Ala, da ke a jahar Benue zuwa wajen yar uwarsa dake a nan Kano, me suna Asma’u Muhammad.
Wakiliyar mu Zulaihat Yusif Aji ta zanta da wannan magidanci, wanda ya bayyana mata yadda wannan al amari ya kasance.
Mal Rabi’u ya kara da cewa wannan al’amari na “Yajin maza” ba sabon abu bane a wajen maza.
Yace bacin rai da yake samu a wajen matansa ko wace rana ya sa shi wannan yaji.
Daga karshe ‘’yar uwar magidancin Asma’u Muhammad wacce ya gudo wajen da take zaune a Kano, ta bayyana yadda al’amarin ya faru inda ta ce zasu mai dashi daga baya, amma se matan sun gyara kuskuransu .