Labaran Wasanni
Wasan kwallon kurket: NCF za ta kaddamar da sabon mai horas wa
Hukumar wasan kwallon kurket ta Najeriya wato NCF ta shirya kaddamar da tsohon dan wasan kasar Sri Lanka Asanka Gurusinha a matsayin sabon mai horas da ‘yan wasan Najeriya a cikin kwanaki masu zuwa.
Gurusinha mai shekara 44 wanda kuma mamba ne da ya taimakawa kasar sa ta Sri Lanka wajen lashe gasar cin kofin duniya a wasan kwallon kurket na shekarar 1996, ana sa ran zuwansa Najeriya don gabatar dashi kan mukamin da hukumar tashi.
Bayan aikin kula da kungiyar wasan kwallon kurket ta kasa, Gurusinha zai kasance cikin masu bayar da horo ga kananan masu horaswa na cikin gida.
Shugaban hukumar ta NCF Yahaya Ukwanya, ya ce, an zabi Gurusinha ne duba da irin gogewar da yake da ita a fagen wasan kurket din don kawo wa Najeriya cigaba a wasanni masu zuwa.
You must be logged in to post a comment Login