Labarai
Wasu dalibai ‘yan asalin jihar Kano da gwamnati ta kasar Masar karatu sun shiga halin garari
Wasu dalibai ‘yan asalin jihar Kano wadanda gwamnatin jiha ta dauki nauyin karatun su a kasar Masar sun roki gwamna Abdullahi Umar Ganduje da ya kawo musu dauki game da mawuyacin halin da suke ciki na rashin kudi.
A wani sako da su ka aikawa gidan rediyo freedom sun ce rabonsu da a aika musu da kudin alawus tun a watan Fabrairun.
Sun ce sun bi dukkannin hanyoyin da suka kamata domin gabatar da korafinsu ga masu ruwa da tsaki kan lamarin ciki har da hukumar ba da tallafin karatu ta jihar Kano wato Scholarship board amma abin ya citura.
Haka kuma daliban sun kara da cewa a yanzu haka suna hannu baka hannu kwarya, inda kadan daga cikin su wadanda iyayensu ke da dan abin hannu ke tallafawa ‘ya’yansu, yayin da su kuma wadanda iyayensu marasa karfi ne ke rayuwar kunci.
Daliban sun ce gashi suna shekarar karshe kuma gashi ba su da kudaden da za su yi amfani da shi wajen gudanar da project, Yayin da kuma wadanda suka kammala karatunsu daga cikin su, ba su da kudin tiketin jirgi da za su dawo gida.