Manyan Labarai
Wasu gidajen Rediyo da Talabijin na Arewacin Najeriya sun yi tir da karin kudin wuta
Wasu gidajen Rediyo da Talabijin na Arewacin Najeriya sun yi tir da karin kashi dari biyu na kudaden wutar lantarki.
Wata majiya ce dai a hukumar kula da kamfanonin wutar lantarki na kasa suka bayyana cewa tsrain karin kudin wutar lantarkin zai fara ne daga watan Afrilun shekarar bana.
Wasu daga cikin masu amfani da wutar lantarki sun bayyana cewa karin kudin wutar lantarkin zai jefa Najeriya cikin wani mataki na matsanancin Talauci da halin kakani kayi
Masu amfani da wutar lantarkin sun kara da cewa gwamnati tayi ko in kula da bukatun ‘’yan Najeriya inda suka kara wutar lantarkin wanda hakan yake nuna rashin tausayin wasu hukumomin gwamnatin tarayya game da halin da ‘’yan Najeriya ke ciki.
Suma gammayyar manyan maaikatan kamfanonin wutar lantarki sun koka game da kara kudin wutar inda suka ce hakan ba zai kawar da matsalolin da bangaren wutar lantarki ke fuskanta ba.