Kiwon Lafiya
Wasu yan bindiga dadi sun kai hari Dandalin shakatawa a jihar Zamfara
A shekaran jiya da daddare ne Wasu ‘yan bindiga suka kai hari dandalin shakatawa a cikin Karamar hukumar Birinin Magaji dake cikin jihar Zamfara,yayin da suka sace mutane 7.
A cewar mai wurin Shakatawar, Sunusi Iliyasu Ishie ya ce ‘yan bindigar sun kai harin ne da misalign karfe 10 na dare, yayin da suka yi garkuwa da mutane 20 a dandalin shakaatawar dake cikin garin Birnin Gwarin, amma kuma daga bisani suka yi awan gaba da mutum 7 daga cikin su.
Sunusi Iliyasu ya kara da cewar, ‘yan bindigar sun ajiye motocin su nisa da dandalin shakatawar kamar suna gudanar da aikin sintiri daga baya kuma sai suke tambayar nan ne dandalin shakatawar Sunusi? Yace dani da wadandan muke wurin sai muka amsa musu da cewa Eh nan ne, a ganin mu, mun dauka jami’an tsaro ne.
Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar SP Muhammad Shehu ya tabatar da afkuwar al’amarin yana mai cewar tuni jami’an ‘yan sanda suka bi byan su, bayan da ta kaddamar da bincike a kan hanyar.