Labarai
WHO ta kaddamar da kwamitin karta-kwana kan COVID-19
Hukumar lafiya ta duniya WHO ta kaddamar da kwamitin kartakwana kan rarababa kayayyakin dakile cutar COVID19 na Majalisar dinkin duniya.
Babban daraktan hukumar Dr, Tedros Ghebreyesus ya sanar da hakan ta cikin sanarwar da ya sanya a shafin sa na Internet bayan kaddamar da kwamitin a birnin Geneva.
Dr, Tedros Ghebreyesus ya ce zai yi amfani da wannan damar wajen godewa babbban sakataren na Majalisar dinkin duniya Antonio Guterres saboda hada kan hukumomin Majalisar dinkin duniya wuri guda don bada gudunmawar su kan dakile cutar Corona a duniya.
A cewar sa a yau ne aka cika kwanaki 100 tun bayan da WHO aka sanar da ita kan bullar cutar ta COVID-19 a kasar China.
Babban darkatan ya kuma abun mamaki ne cikin kankanin lokaci duniya ta sauya kan wannan mumunan cutar.
You must be logged in to post a comment Login