Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Najeriya na gab da dakile cutar Polio – WHO

Published

on

Hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta ce Najeriya na gab da dakile cutar shan-inna, bayan da ta tattara bayanai game da halin da kasar ke ciki kan cutar ta Polio.

Hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana hakan ne a shafinta na Twitter mallakar ofishinta da ke Brazzaville na kasar Congo, @WHOAFRO.

“A yau, sashen bada shaida na ofishinmu da ke kula da yankin Afirka kan yadda aka dakile cutuka ya karbi takardar tattara bayanan da Najeriya ta gabatar masa.

“Wannan wata rana ce mai muhimmanci ga Najeriya, Afirka da kuma shirin yaki da cutar Polio a Duniya,” in ji WHO.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!