Coronavirus
WHO : Za mu yi bincike kan rigakafin Corona da Rasha ta samar

Hukumar lafiya ta Duniya WHO ta ce sai ta yi kwakkwaran nazari kan ingancin allurar cutar corona da kasar Rasha ta yi ikirarin samarwa kafin sahale masa.
A yau talata ne dai kasar ta Rasha ta sanar da cewa ta kirkiro da allurar cutar ta covid-19.
Mai magana da yawun hukumar ta WHO Tarik Jasarevic, ya sahidawa manema labarai yau a birnin Geneva da ke kasar Switzerland da cewa, tuni suka tuntubi hukumomin kasar ta Rasha don tabbatar da ingancin allurar rigakafin.
Ya ce duk wani magani da za a samar a duniya wajibi ne hukumar ta tabbatar da inagncinsa kafin fara amfani da shi.
Tun farko dai kasar ta Rasha ta yi ikirarin cewa an kirkiro da allurar cutar ta covid-19 ne a cibiyar bincike ta Gamaleya
You must be logged in to post a comment Login