Labarai
WHO:Najeriya na daf da fita daga jeren kasashen masu cutar shan-inna
Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce nan ba da jimawa ba za ta ayyana Najeriya a matsayin kasar da babu cutar shan-inna wato Polio.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban jami’in yada labaran hukumar a Najeriya Mr Charity Warrington ya fitar jiya a Abuja, a madadin babban jami’in hukumr a kasar nan Mr Clement Peter.
Sanarwar ta yi Karin hasken cewa Mr Peter ya ce matukar ba a samu bullar cutar a cikin watanni biyu masu zuwa ba, to kasar nan za ta cika shekaru 3 cur kenan babu cutar kuma ta cika ka’idar da ta hukumar ta WHO ta ware don ayyana ta a matsayin kasar da babu Polio.
Haka zaliki ya yabawa mahukuntan kasar nan bisa jajircewarsu wajen wayar da kan al’umma don karbar allurer rigakafin cutar, wanda hakan ya haifar da gagarumar nasara.
Sai dai ya bayyana tashe-tashen hankulan da ake fuskanta a yankin Arewa-maso gabashin kasar nan a matsayin babban kalubalen da suke fuskanta, da ya yi fatan samun cikakken zaman lafiya don inganta lafiyar al’ummar kasar nan.