Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

World Cup 2022: Saura zagaye Daya Portugal ta Kai gasar kofin duniya

Published

on

Tawagar kasar Portugal tayi nasar doke kasar Turkiyya da ci 3 da 1 a wasan share fagen shiga gasar cin kofin duniya na shekarar 2022 a kasar Qatar.

Kasar Portugal tayi nasar ne bayan Kai Ruwa Rana tsakanin kasashen biyu sukai , wasan da ya gudana a ranar Alhamis 24 ga Maris din da muke cikin a filin wasa na Estadio de Dragao.

Dan wasa Otavio ne ya fara zura kwallon farko a minti na 15, kafin Diego Jota ya fara zura kwallo ta biyu a minti na 42 dab da za a je hutun rabin lokaci.

Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci a minti na 65 dan wasa Burak Yilmiz ya zura kwallo a ragar kasarsa ta Turkiyya da wasan ya zama 2 da 1.

Ronaldo

Sai dai a minti na 85 dan wasa Burak Yilmiz ya barar da kwallo a bugun daga kai sai mai tsaran gida a wasan.

Kana mintina kadan a kamalla wasan dan wasa Matheus Luiz ya tabbatar da nasarar kasar Portugal a wasan da da ci 3 da 1 bayan kwallo da ya zura a minta na 90.

Kawo yanzu dai kasar Portugal mataki daya ya rage mata wanda idan tayi nasara to zata buga gasar cin kofin duniya na shekarar 2022 da muke ciki a kasar Qatar.

Inda Portugal din zata kece raini da kasar Macedonia ta arewa bayan da kasar ta doke Italiya a wasan da suka fafata a ranar Alhamis.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!