Labarai
Ya kamata al’umma su rinka tallafawa daurarru a gidajen gyaran hali – Tsohon kwamishina
Kungiyar tsoffin daliban Kwalejin garin Keffi da ke Jihar Nassarawa ta yi kira ga al’umma musamman masu hannu da shuni da su rinka tunawa da daurarrun da ke gidajen gyaran hali a ko da yaushe, ta hanyar tallafa musu da kayan masarufi da na harkokin yau da kullum.
Shugaban kungiyar reshen Jihar Kano kuma tsohon Kwamishinan harkokin noma a mulkin soja da na ilimi a mulkin farar hula Alhaji Musa Salihu ne ya bayyana hakan yayin mika kayan tallafi ga mazauna gidan gyaran hali na Kurmawa da ke nan Kano.
Alhaji Musa Salihu ya kara da cewa shekara da shekaru kenan suna aiwatar da irin wannan aiki na rabon kayan tallafi ga al’umma.
A na sa bangaren sakataren kungiyar Farfesa Mustapha Muhammad na Jami’ar Bayero da ke nan Kano, ya ce, “Muna taimakawa tsohuwar makarantar tamu ne da kuma sauran bangarori na rayuwar al’umma domin zaburar da na bayanmu kan ayyukan alheri.”
Kayayyakin da Kungiyar ta kai gidan gyran halin na kurmawa sun hada da sukari da mangirki da fulawa da sinadarin dandanon girki da takalma da audugar mata da ruwan sha na robobi da na leda da sauransu.
You must be logged in to post a comment Login