Ƙetare
Ya kamata Bola Tinubu yayi taka tsan-tsan wajen yankewa Nijar hukunci- Gamayyar ƙwararru ta Nijeriya
Gamayyar ƙwararrun a Nijeriya ta yi kira ga Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi taka-tsantsan wajen ɗaukar matakan mayar da jamhuriyar Nijar kan turbar dimokraɗiyya, bayan juyin mulkin da sojoji suka yi wa shugaba Mohamed Bazoum.
A wata buɗaɗɗiyar wasiƙa da gamayyar ta aika wa Shugaba Tinubu, ta ce akwai buƙatar kasar nan ta zamo mai sara tana duban bakin gatari game da matsayarta a kan abin da ke faruwa a Nijar, musamman bisa la’akari da daɗaɗɗiyar dangantaka mai kyau tsakanin ƙasashen biyu, aminan juna.
Shugaban kasa, Bola Tinubu, shi ne ke jagorantar Ƙungiyar Raya Ƙasashen Afirka ta Yamma wato Ecowas da ta bai wa sojoji masu mulki a Nijar wa’adin kwana bakwai, don su mayar da mulki hannun hamɓararren shugaban ƙasa Bazoum Mohamed ko kuma ta ɗauki matakin amfani da ƙarfi a kansu.
Gamayyar wadda ta ƙunshi ƙwararru daga ɓangarori daban-daban na rayuwa, ta bi sahun Ecowas da sauran ƙasashen da ƙungiyoyin duniya wajen yin Allah-wadai da juyin mulkin na Nijar, amma ta ce hanyar lumana ta fi dacewa a bi wajen warware matsalar.
You must be logged in to post a comment Login