Kasuwanci
Ya kamata matasa su dage wajen koyon dabarun kasuwancin zamani – NCC
Shugaban hukumar sadarwa ta ƙasa NCC, Farfesa Umar Garba Ɗanbatta ya buƙaci matasan da aka bai wa horon dabarun kasuwancin zamani da su alkinta ilimin da suka samu ta hanyar da ta dace.
Farfesa Ɗanbatta ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi ga waɗanda suka samu kyautar kayayyakin gudanar da kasuwancin ta kafafen sadarwa bayan kammala horon.
“Ya kamata matasan mu su mayar da hankali wajen koyon ilimin kasuwancin zamani don ganin sun zamo masu dogaro da kansu,” in ji shi.
A nasa jawabin shugaban makarantar Digital Bridge Institute, Farfesa Muhammad Ajiya, ya ce an horar da matasa dabaru iri-iri har da na shugabanci da zai taimaka musu wajen cimma burinsu a rayuwa.
You must be logged in to post a comment Login