Labaran Kano
Ya wajaba al’ummar mu su bunkasa tattalin arzikin Kano- Oba Ewuarin
Sarkin masauratar al’ummar Benin Oba Ewuarin Ogidigan na biyu ya ja hankalin al’ummar masarautar Edo mazauna Kano da su himmatu wajen kawo cigaban ta fuskar tattalin arzikin jihar Kano.
Ewuarin Ogidigan ya bayyana hakan ne yayin wani taron al’mmar jihar Edo mazauna jihar Kano a yau.
Ya ce shakka alaka tsakanin jihar Kano da Edo dadaddiya ce, da ta haifar da alfanu a tsakanin jihohin biyu.
A yayin taron ‘Yan Dakan Kano, Alhaji Abbas Muhammad Dalhatu ne ya wakilci Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu.
Taron al’ummar jihar Edo karkashin masarautar Benin ya samu halartar al’ummar masarautar Benin mazauna jihar Kano, da sauran ‘yan majalisar Sarkin na Benin.
Wakilin mu Shamsu Dau Abdullahi ya rawaito cewa, Masarautar Benin ta samu asali ne tun shekaru 900 da suka shude, da yanzu take karkashin jihar Edo.
Galibi dai a wadancan shekaru masarautar tayi sarakuna da suka yi shura a bangarori daban-daban na rayuwar al’umma.
Yankin da sarakunan suke yin shugabanci a baya, ya kasance mai dinbim tattalin arzikin karkashin kasa da albarkatun noma.