Kiwon Lafiya
Alhaji Ado Muhammad:ya nuna damuwarsa dangane da tabarbarewar tattalin arzikin jihar Kano
Mataimakin shugaban cibiyar habbaka tattalin arzikin jihar Kano kuma shugaban gudanarwar rukunin gidajen Rediyon Freedom Alhaji Ado Muhammad, ya nuna damuwar sa dangane da tabarbarewar tattalin arziki a jihar Kano da ma jihohin Arewacin Najeriya.
Alhaji Ado Muhammad ya furta hakan ne yayin da cibiyar ke zaman tattauna mafita ga matsalar tattalin arziki da yake barazana da rayuwar al’ummar wannan yanki.
Ya kuma ce hakan na jawo lalacewar tarbiyyar matasan wannan zamani.
Ya ce ya zama wajibi masu arzikin dake cikin wannan al’umma su fito da tsarin da za su rinka taimakawa matasa da dabarun ayyukan yi, da kuma jarin sana’oin da zasu rayu.
Shugaban cibiyar Alhaji Sa’id Dattijo Adhama yana horon al’ummar wannan yanki da su kasance masu kamanta gaskiya a cikin harkokin su a matsayin wani kadarkon kawo albarka a cikin al’amuran su.
A nasa bangaren, wani sanannan Dan kasuwa Alhaji Abba Garba Karfe ya ce, za su bada gudunmawar da ta dace wajen ci-gaba da baiwa matasa yanayin da zasu yi sana’o’i don ci gaban rayuwar su.
Shugaban cibiyar Alhaji Sa’id Dattijo Adhama ya yi kira ga al’ummar wannan yanki na Arewa da su kasance masu kamanta gaskiya a cikin harkokin su a matsayin wani kadarkon kawo albarka a cikin al’amuran su.