Labarai
Yadda aka ceto wasu mutane a hannun ‘yan Boko Haram
Rundunar sojin kasar nan ta mikawa gwamnatin jihar Borno wasu mutane dari da shida wadanda suka tsere daga hannun kungiyar Boko Haram.
Hakan na cikin wata sanarwa ce da gwamnatin jihar Borno ta fitar a shafinta na Internet.
Sanarwar ta ce mutanen sun tsere ne daga hannun Boko Haram inda suka fada hannnun dakarun kasar nan.
A cewar sanarwar casa’in da hudu daga cikin mutanen wadanda suka hada da maza magidanta 37 da mata 17 da kuma kananan yara 40 ‘yan Najeriya yayin da sauran kuma ‘yan kasashen Chadi ne da Kamaru.
You must be logged in to post a comment Login