Manyan Labarai
Yadda ake maganin cutar sankarar mama
Tsotson nonon mata da mazan su zasu yi ,na taimakawa kwarai da gaske wajen gano cutar daji da aka fi sani da Cancer dake kama maman matan.
Mai bincike mai suna Abigael Shona tace tsotsar nonan matan da maza zasu yi yana taimakawa wajen bibiyar cutar cancer daka iya shafar nonan na mata.
Abigael ta kara da cewa iyayen da suke shayar da nono na daga cikin wadanda ke kasa da kamuwa da cutar ta daji kafin da bayan sun daina yin jini.
Yawancin matan da ke shayar da nonan suna iya fuskantar canji a wasu sassan jikinsu lokacin da suke shayarwa wanda hakan ke kawo jinkiri na al’ada.
Saboda haka tsotsar nono da namiji ka iya yi, shine gano cutar ta daji a jikin nonuwan mata tare da jin kumburin akan lokaci domin neman taimakon likita.
Abigael ta kara da cewa abun da ya kamata ne a karfafawa mata gwiwa su rika barin mazajen su suna mammatsa nonuwan su ,domin gane cutar daji akan kari.
Saboda haka kada mata su hana mazajensu jin dadin tsotsar nono da jujjuya shi domin hakan na matukar amfani ga matan.
“Masaniyar da ta yi binciken tace gano maganin cutar dajin mama da wuri abu ne mai kyau saboda mata da dama basa yin hakan.
Saboda haka idan suka bar mazan su, suka taimaka wajen wasanni da nonuwan babbar hanya ce ta maganin cutar ta dajin mama.
Bayanan sun bayyana cewa idan aka gano cutar kafin ta kara ruruwa za’a iya tsira daga illolinta.
Kwararriyar maaikaciyar lafiyar ta kara da cewa maza ma na iya kamuwa da cutar ta daji ,sannan sun bayar da shawara da su lura sosai domin maganin kamuwa daga cutar.