Coronavirus
Yadda dokar kulle ke gudana a Jigawa
Tun bayan bullar cutar Coronavirus cikin watan Afrilu na wannan shekara ta 2020 a jihar Jigawa, gwamnatin jihar ta ci gaba da daukar matakan kariya, domin yakar cutar da dakile ta, kamar dai yadda sauran wuraran da cutar ta bulla sukeyi.
To sai dai da a’lama dokar zaman gida tafi yin tasiri a bangarori da dama na jihar, kama daga kaura cewa cunkoson mutane a gidan biki ko suna, dama kasuwanni kamar yadda wani dan kasuwa ya ke fayyace mana a nasu bangare.
Karin labarai:
Covid-19: Mutum na 3 ya rasu sanadiyyar Corona a Jigawa
Covid-19: Gwamnatin Jigawa ta fara rabawa likitocin Corona N10,000 a kullum
Koda shima wani magidanci Saminu Engineer mai gyaran motoci yace dokar Lockdown ta mayar dashi sai yayi roron masara an biyashi yake samun na kalace, tun da yanzu babu sufuri balle ya samu gyara, a wani gefen kuma ga nauyin iyalin da kullum idon su a kansa.
Suma mata iyayen gida sunce tasirin wannan doka hadda su bawai iya magidan tane kadai ba.
Sukuwa ulama’u magada annabawa sunci gaba da fadawa al’umma suyi koyi da halin manzo wato dai hakuri.
You must be logged in to post a comment Login