Labarai
An baiwa Dan sarauniya sabon mukami a gwamnati
Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya nada dakataccen kwamishinan ayyuka da raya birane Injiniya Mu’azu Magaji a matsayin shugaban kwamitin kula da aikin shimfida bututun iskar Gas na gwamnatin Kano.
Hakan na cikin sanarwar da babbar sakatariyar bincike da lura da al’amuran siyasa ta ofishin sakataren gwamnatin Kano Hajiya Bilkisu Shehu Maimota ta fitar a yau Alhamis.
Idan za a iya tunawa dai, a watan Afrilun shekarar da muke ciki ne gwamna Ganduje ya dakatar da Mu’azu Dan sarauniya biyo bayan wasu kamalami da ya yi kan shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa marigayi Malam Abba Kyari.
You must be logged in to post a comment Login