Labaran Kano
Yadda Ganduje ya biyawa daliban Kano kudin NECO
Gwamnatin jihar Kano ta biya kimanin naira miliyan 50 ga hukumar shirya jarrabawar kammala sakandare ta kasa NECO domin sakin sakamakon jarrabawar daliban jihar Kano.
Kwamishinan ilimi na jihar Kano Muhammad Sanusi kiru ya bayyana hakan ne a jiya ya yin zantawa da manema labarai a fadar gwamnatin Kano
Muhammadu Sanusi Kiru ya Kara da cewa a jiya hukumar ta aiko da racitin Remita Wanda a yau gwamnatin ta biya kudin.
Wakiliyar mu Zahrau Nasir ta ruwaito cewa, Kwamishinan ya ce za’a saki sakamakon nan bada jimawa ba.
You must be logged in to post a comment Login