Manyan Labarai
Yadda Gwamnonin Jihar Kano suka aiwatar da ayyukan raya kasa.
Tun sanda aka kirkiri jihar Kano ranar 27 ga watan Mayu na shekarar 1967 kimanin shekaru 52 kenan jihar ta Kano ke fuskantar kalubale da nasarori na shugabanci.
Bayan kirkirar jihar Kano zamanin mulkin tsohon shugaban kasa Janar Yakubu Gowon aka turo Marigayi Kwamishinan Yansanda Marigayi Alhaji Audu Bako a matsayin Gwamnan jihar Kano na farko.
Marigayi Audu Bako ya Mulki jihar Kano na kusan tsawon shekaru 9 har zuwa sanda Janar Murtala ya tumubuke gwamnatin Janar Yakubu Gowon.
Duk irin abubuwan da jihar Kano ke takama da shi a yanzu ana alakanta shi ne da mulkin Marigayi Alhaji Audu Bako da ya hada da madatsar ruwa ta Tiga, kimanin shekaru hamsin al’ummar Kano na amfana da wannan madatsar ruwa domin yin noman rani.
Sai Gwamnan Kano na biyu Kanar Sani Bello wanda ya ka kafa makarantun kimiyya da fasaha na Dawakin kudu da Dawakin Tofa, wadannan makarantu al’ummar Jihar Kano na alfahari da su wanda sakamakon haka ‘yan asalin jihar Kano dake sassan Duniya sun zama manyan likitoci.
Sai Gwamna Ishaya Aboi Shekari da ya dubi yadda aka mika Mulki daga hannun soja zuwa farar hula.
A ranar daya ga watan Oktoban shekarar 1979 Najeriya ta dawo turbar dumukradiyya inda sojoji suka mika Mulki ga farar hula , a tsohuwar Jihar Kano wacce take hade da Jihar Jigawa ta yanzu Marigayi Alhaji Muhammadu Abubakar Rimi ne ya zama gwamnan Jihar Kano.
Zaman Alhaji Muhammadu Abubakar Rimi Gwamnan Jihar Kano ya saka tsohuwar Jihar Kano ta samu sauye sauye a tsawon shekaru hudu da yayi yana mulkin tsohuwar jihar ta Kano.
Daga cikin nasarorin da gwamna Muhammadu Abubakar Rimi ya samu akwai gina makarantun sakandire fiye da dari biyu a fadin jihar Kano da Jigawa ta yanzu ,da kai wutar lantarki zuwa lokuna da sako na jihar Kano da ya hada da kauyuka.
Rahotanni na nuni da cewa mafi yawa daga cikin wasu kauyuka da Marigayi Alhaji Muhammadu Abubakar Rimi ya kai wutar lantarki har yanzu Falwayoyin su suna nan kuma ana aiki da su yadda ya kamata.
Bayan marigayi Alhaji Abubakar Rimi ya kammala wa’adin mulkin sa ne aka yi zabe sai Marigayi Alhaji Sabo Bakin Zuwo ya karbi Mulki.
Amma akwai wani abu da ba’a taba yiba wata uku kafin zabe marigayi Alhaji Muhammadu Abubakar Rimi ya sauka daga mukamin Gwamna inda ya nada mataimakin sa Marigayi Alhaji Abdu Dawakin Tofa.
Bayan Alhaji Sabo Bakin Zuwo ya karbi gwamnati a ranar 1 ga watan Oktoban 1983 ne wata uku rak yana kan karaga sai sojoji suka yi juyin Mulki.
Daga baya gwamnonin mulkin soja sun biyo baya irin su Air Vice Marshal Hamza Abdullahi da Kanal Ahmad Muhammad Daku sai Group Captain Muhammadu Ndatsu Umaru da Kanal Idris Garba.
A watan Janairun shekarar 1992 ne Kanal Idris Garba ya mika Mulki ga Alhaji Kabiru Ibrahim Gaya wadda Gwamnatin sa bata dade ba wanda ya sauka a ranar 18 ga watan Nuwambar shekarar 1993 bayan Janar Sani Abacha ya tumbuke gwamnatin rikon kwarya ta Cif Ernest Shonekan.
Daga nan ne aka nada kantomomin mulkin soja irin su Marigayi Kanal Muhammadu Abdullahi Wase da Kanal Dominic Obukudata Oneya da Kanal Aminu Isa Kontagora.
Amma a ranar 29 ga watan May una shekarar 1999 Kanal Aminu Isa Kontagora ya mika Mulki ga Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso a filin wasa na Sani Abacha.
Karbar mulki da Rabiu Musa Kwankwaso yayi ke da wuya ya fara ayyukan raya kasa da suka hada da jona wutar lantarki a kauyukan jihar Kano da fito da shirin CRC da ciyar da daliban makarantun Firamare da daukar ‘yan asalin jihar Kano.
Rabiu Musa Kwankwaso ya dauki masu shedar takaddun digiri su dubu daya aiki a gwamnati.
Bayan faduwar Rabiu Musa Kwankwaso gwamnan Jihar Kano Malam Ibrahim Shekarau ya karbi gwamnati a ranar 29 ga watan Mayu na shekarar 2003 ya fito da tsare tsare kamar gyara titunan jihar Kano dake birni da kauyuka da daukar nauyin matasa a taimakon marasa karfi.
Bayan saukar Malam Ibrahim Shekarau a ranar 29 ga watan Mayu na shekarar 2011 Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso ya sake dawowa mulkin jihar Kano inda ya gaji Malam Ibrahim Shekarau ,Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso ne ya fara yiwa birnin Kano gadar sama da motoci zasu rika hawa da tura matasa kimanin dubu biyu kasashen waje domin yin karatun digiri na biyu.
Magajin injiniya Rabiu Musa Kwankwaso kuma gwamnan Kano mai ci a yanzu Dr Abdullahi Umar Ganduje ya dora akan ayyukan da inijinya Rabiu Musa Kwankwaso yayi.
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje shi ma ya kirkiri nasa ayyukan kamar gadar kasa ta hanyar Pansheka ta Titin Sheikh Jafar sai Kuma gadar kasa dake kofar ruwa da sauran su.
Ko yaya al’ummar Kano zasu yiwa gwamnonin su alkalanci ?