Labarai
Yadda kungiyar JUHESU ta janye yajin aiki a Najeriya
kungiyar ma’aikatan lafiya ta kasa JUHESU ta janye yajin aikin mako guda da ta tsunduma a baya-bayan nan, tare da bukatar mambobinta da su gaggauta komawa bakin aikin su daga yau Litinin 21 ga watan satumbar nan da muke ciki.
Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar a daren jiya Lahadi mai dauke da sa hannun shugabanta na kasa Comrade Bio-bé-ken-tóye Toy Josiah.
Ta cikin sanarwar kungiyar ta bayyana cewa ta janye yajin aikin ne duba da cewa gwamnatin tarayya ba ta biya musu bukatun su ba, sai dai ta ce nan gaba kadan kwamitin zartarwar na kungiyar zai yanke hukuncin da za a dauka a nan gaba.
Idan ba a manta ba a ranar 13 ga watan nan na Satumba ne kungiyar ta tsunduma yajin aikin gargadi na kwanaki bakwai sakamakon rashin biya musu bukatun su ciki har da rashin biyan su kudaden alawus alawus na aikin hatsarin annobar Corona da Suka yi.
You must be logged in to post a comment Login