Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kano: Yadda Ma’aikatan FAAN suka yi rusau a Aviation Quaters

Published

on

Mazauna gidajen ma’aikatan hukumar filin jirgin sama watau Aviation Quarters da ke nan Kano, sun bukaci gwamnatin tarayya da ta shiga tsakanin su da hukumar filin jirgin saman Malam Aminu Kano FAAN bisa yunƙurinta na tashin su daga gidajen da suke ciki bayan da gwamnatin tarayya ta sayar musu da gidajen.

Sakataren ƙungiyar mazauna rukunin gidajen na Aviation Quarters Obadaki Muhammad Mustapha, ya buƙaci hakan yau Laraba yayin da shugabannin ma’aikatan filin jirgin na FAAN suka shiga rukunin gidajen tare rushe wasu gine-gine da wadanda suka sayi gidajen a hannun kwamitin gwamnatin tarayya suka fara yi.

Haka kuma ya ce, tuni wasu daga cikinsu suka kammala biyan kudin ga kwamitin Gwamnatin tarayya na sayar wa ma’aikatan gidajen da suke ciki, inda hukumar NiMet da NAMA suka aminta da sayar wa ma’aikatan nasu gidajen, yai da ita kuma FAAN ta ki amincewa da wannan ciniki, inda ta ce gidajenta ne kuma ba a sanar da su batun sayarwar ba.

Obadaki Muhammad Mustapha, ya kara da cewa, ” Ma’aikatan hukumomi uku ne ke zaune a wurin nan, Akwai ma’aikatan hukumar NAMA da na hukumar NiMet da kuma ma’aikatan hukumar FAAN, kuma duk kowanne ya ci gajiyar sayar masa da wadannan gidaje, sai dai ita hukuma FAAN ta ki amincewa da wannan tsari wanda hakan ke zama babbar barazana a garemu, duk da cewa mun biya kudi an bamu shaidar mallaka kuma kowa an nuna masa iyakar wurinsa”.

Sai dai a nasa bangaren, muƙaddashin shugaban hukumar kula da filayen jirgi na Malam Aminu Kano Ahmad Danjuma, ya ce, ba su da maaaniyar sayar da gidajen a hukumance, don haka suka dauki matakin hana ƙara gini ko kuma sake sayar da su ga wasu.

Ahmad Danjuma, ya ce, ” Mun rubuta musu gargadi a takarda har sau uku kan su dakatar da yin gini ko kuma sayar da gidajen ga wasu mutane na waje, amma suka ki, don haka muka dauki matakin yin rusau tunda dama mun sanar da su daukar wannan mataki a rubuce”.

Shugaban filin jirgin na Aminu Kano, ya ƙara da cewa shi ma ya karɓi umarni ne daga shalkwatar hukumar FAAN ta ƙasa domin kulawa da ƙadarorin hukumar.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!