Labaran Kano
Yadda mahaifi ya daure ‘yarsa tsawon wata guda a Kano
Wani magidanci mai suna Sani Dayyabu mazaunin unguwar Sheka Aci Lafiya, dake nan Kano, ya daure ‘yarsa mai suna Nafisatu Sani ‘yar kimanin shekara 18 a mari, har tsawon wata guda.
Ana zargin mahaifin ya daureta ne acikin wani daki dake gidansa saboda yawace-yawacen da yace tana yi, dukda cewa tana da larurar tabin hankali.
Sai dai matashiyar Nafisatu Sani ta bayyanawa Freedom Radio cewa mahaifinta ya jima yana dukanta, inda har ta kai ya karya mata hannu, hakan yasa ta tafi gidan kakarta inda tayi jiya a can.
Bayan dawowarta gidan ne sai mahaifinta Sani Dayyabu yayi mata duka sannan ya sanyata a mari ya kuma kulleta a cikin daki.
Freedom Radio tayi kokarin jin ta bakin mahaifin na ta, amma yace sam ba zaiyi magana da ‘yan jaridu ba.
Wakilinmu Yakubu Musa Kanwa ya rawaito mana cewa shugaban kungiyar kare hakkin dan adam Karibu Yahya Lawal Kabara ya ce tuni suna cigaba da bincike kan wannan al’amari domin daukar matakin da ya dace.
Labarai masu alaka:
Mutumin da ya daure ‘ya’yan sa shekaru 3 a Kano ya rasu a Asibiti