Labarai
Yadda Maniyyata Hajjin bana na jihar Nasarawa suka gamu da hatsarin mota

Maniyyatan aikin Hajjin bana na jihar Nasarawa da ke shirin tashi a jirgin farko, sun yi hatsarin mota.
Rahotonni sun ce mutane hudu sun samu rauni bayan da motar maniyyatan ta yi fadi da su da yammacin Larabar makon nan a hanyarsu ta zuwa Abuja inda za su hau jirgi.
Maniyyatan sun yi hatsarin ne a cikin mota kirar bas mai daukar mutane 18 a yankin karamar hukumar Keffi a ta jihar.
You must be logged in to post a comment Login