Labaran Kano
Yadda matashi ya rasa ransa a hannun ‘yan sanda
Tun a farko dai wani rikici ne ya faru tsakanin marigayin Abba Abdulkadir da wani a garin Madobi, inda yayi karar sa a wurin ‘yan sanda, sai dai basu samu kamo shi ba, mahaifinsa ya kai musu shi kafa da kafa.
Sai dai hakan a iya cewa ya bar baya da kura domin kuwa da zuwan mahaifin sai suka fara marin marigayin, a karshe dai ya rasa ransa sanadiyyar dukan da yasha a hannun ‘yan sandan, bayan da ya rama marin da guda daga cikin ‘yan sanda yayi masa.
‘Yan uwan marigayin sunyi kokarin kai shi asibiti a lokacin da ya gabata amma su kaje har asibitoci guda biyu sai dai aka ki karbarsu sakamakon halin da yake ciki, kasancewar ana bukatar saida sa hannun ‘yan sanda.
A karshe sun samu daya daga cikin ‘yan sandan wanda ya amince aka tafi dashi zuwa asibitin Murtala bayan da suka baiwa wani dan sanda cin hanci na Naira dubu takwas ya kaiwa DPO, don samun damar kaishi asibitin, wanda a can ne kuma rai yayi halinsa.
Kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano DSP. Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatarwa da Freedom Radio cewa tuni rundunar su ta samu wannan labari kuma sun cafke wadannan ‘yan sanda da ake zargi da aikata wannan mumunan laifi.
Sannan kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano CP. Ahmed Iliyasu ya bada umarnin sauya DPO ‘yan sanda na garin Madobin, yayin da kuma aka tarwatsa ofishin na Madobi wajen sauyawa jami’an ‘yan sanda wuraren aiki saboda kaurin suna da ofishin yayi na karbar kudin bele da kuma cin hanci da rashawa
Suma a nasu bangaren wasu gungun lauyoyi masu kishin al’umma sun ce sun shirya tsaf domin kwatowa wannan matashi hakkinsa, a tattaunawar da Freedom Radio tayi da daya daga cikin lauyoyin Barista Abba Hikima Fagge ya bayyana mana cewa babu inda doka ta baiwa dan sanda damar ya doki farar hula, ko ya dauki hukunci a hannun sa.
Rubutu Masu Alaka:
‘Yan sanda sun cafke sojoji kan KAROTA
‘Yan sanda sun yiwa mutanen Bichi alkawari