Labarai
Yadda ‘yan sanda suka kama wanda ake zargi da alaka da ‘yan bindiga a Katsina
Rundunar ‘yan sanda a jihar Katsina ta kama wani tsohon shugaban riko na karamar hukumar Jibia Haruna Musa Mota da ake zargin yana da alaka da ‘yan bindiga kuma yake aikata ta’asa a jihar.
Mai magana da yawun rundunar Gambo Isah ne ya bayyana haka ya yin zantawa da manema labarai.
Ya ce an kama tsohon shugaban riko na karamar hukumar ta Jibia ne sakamakon yadda yake taimaka wa wajen aikata ayyukan ta’addanci a jihar.
Ya kuma ce tuni an gurfanar da shi a gaban kotu don girbar abin da ya shuka.
Rubutu masu alaka
Babban sufeton ‘yan Najeriya ya gana da manyan jami’an ‘yan sanda
Mun cafke masu safarar makamai a Katsina – ‘Yan sanda
An maida yaran da aka sace daga jihar Gombe zuwa Anambra – ‘Yan sanda
Rahotanni sun ce me yiwuwa rundunar ta kama Haruna Musa Mota ne sakamakon yadda aka ji muryarsa cikin wani fefen murya yana tattaunawa da ‘yan bindiga da suka sace daliban sakandieren kankara a watan Disamban shekarar da ta gabata.
You must be logged in to post a comment Login