Labarai
Yadda ‘yan sanda suka kama wasu mutane da ake zargin yi wa yarinya fyade a jihar Yobe
Rundunar ‘Yansandan jihar Yobe ta kama wasu karti 3 da ake zargi sun yiwa wata karamar yarinya ‘yarshekara 13 fyade na taron dangi a garin Potiskum.
Kakakin rundunar ASP Dungus Abdulkarim ya ce matasan sun yi amfani ne da lokacin bikin kirsimeti wajen keta haddin yarinyar.
Haka kuma ya ce rundunar na tsare da wani mutum mai suna Bako Umaru, mai shekaru 35 bisa zargin yin garkuwa da kuma yiwa wata yarinya fiyade , har ma ya jima ta rauni, a Unguwar Hausari dake Geidam.
You must be logged in to post a comment Login