Coronavirus
Yadda yawan masu dauke da cutar Corona suka karu a Najeriya – NCDC
Hukumar dakile yaduwar cututtuka ta kasa NCDC tabbatar da samun karin mutane 124 masu fama da Coronavirus a jiya Alhamis.
Hukumar ta bayyana hakan ne a shafin ta na Twitter kamar yadda ta saba a kowacce rana, tana mai cewa a yanzu haka akwai mutane dubu 54,588 cikin su kuma guda 42,627 da suka warke daga cutar, yayin da dubu 1,048 suka hallaka a dalilin cutar.
Anan Kano dai ma’aikatar lafiya ta ta jiha, ta ce ba’a sami karin mutum ko da guda guda da ya kamu da cutar, a jiya Alhamis din ba, tana mai cewa a yanzu haka mutane dubu 1, 737 suka kamu da cutar, cikin su kuma guda 1,591 sun warke, sai kuma mutane 54 da suka hallaka dalilin cutar.
Yanzu haka masu corona 82 kadai suka rage wadanda ke jiyyar cutar a nan Kano.
Jihar Katsina kuwa ta sami karin mutane 14 masu dauke da cutar, inda yanzu take da yawan mutane 810 masu dauke da cutar cikin su kuma 457 sun warke sai kuma guda 24 da suka rasa ransu dalilin cutar.
You must be logged in to post a comment Login