Labarai
Yadda zaman majalisar dokokin Kano ya kasance a yau
Wannan dai shi ne zama na biyu tun bayan dawo daga zaman gida ko dokar kulle tun lokacin da aka samu bullar cutar Corona a jihar Kano.
Majalisar dai ta kwashe fiye da watanni 3 a garkame kasancewar gwamnatin Kano ta dauki matakin dakile cutar ta COVID-19.
Akasarin ‘yan majalisar sun halacci zaman majalisar na yau, wanda dama wasu ke ganin cewar hakan ba zai rasa nasaba da zaman kulle da aka jima ana yi ba a nan Kano.
A yayin zaman majalisar na yau Litinin bayan karanta rahoton kwamitin kula da al’amuran zabe na majalisar ta sahalewa gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje ya nada Malam Ahmad Rufai Yalwa a matsayin Kwamishina a hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kano KANSIEC.
Da yake gabatar da rahoton kwamitin tantance shi, Shugaban kwamitin kula da al’amuran zabe na majalisar Tasi’u Ibrahim Zabainawa, ya ce binciken da suka gudanar akan Malam Ahmad Yalwa, ya nuna cewa mutum ne jajirtacce a akan ayyukan da ya gudanar a baya.
Labarai masu nasaba:
Majalisar dokokin Kano ta dawo daga hutu
Majalisar dokokin Kano ta dakatar da manbobin ta guda 5
Kazalika majalisar ta nemi gwamnatin jihar Kano ta daga darajar Asibitin kula da lafiya a matakin farko dake garin Zarewa a karamar hukumar Rogo zuwa matakin babban Asibiti.
Bukatar hakan ta biyo bayan kudirin da Dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar ta Rogo a majalisar Magaji Hamisu Zarewa ya gabatar gaban zauren majalisar a zamanta na yau Litinin.
Da yake gabatar da kudirin Magaji Hamisu Zarewa ya ce, yanzu haka al’ummar da ke ziyartar asibitin sun yi matukar haura adadin wadanda ya kamata su rika zuwa.
Haka shi ma dan majalisa mai wakiltar kananan hukumomin Kura da Garun Malam Hayatu Musa Dorawar Sallau, ya gabatar da kudirin neman a gina Titin da ya tashi daga garin Dan Hassan mai tsawon Kilo mita 22 wadda ta dade da lalacewa, yana mai cewa idan aka gina hanyar za ta taimaka matuka wajen bunkasa tattalin arzikin da ma na jihar Kano baki daya.
Wakilinmu na majalisar dokokin ta jihar Kano Auwal Hassan Fagge, ya ruwaito cewa a makon da ya gabata ne majalisar ta dawo zamanta a yayin da kotu ta bada umarnin janye dakatarwar da majalisar ta yiwa wasu daga cikin mambobin ta.
You must be logged in to post a comment Login