Kiwon Lafiya
Yajin aiki: An cimma matsaya tsakanin ƙungiyar NARD da gwamnatin tarayya
Gwamnatin tarayya ta cimma matsaya da ƙungiyar likitoci masu neman ƙwarewa ta ƙasa NARD, kan batun janye yajin aikin da suka tsunduma makwanni biyu da suka gabata.
Rahotanni sun bayyana cewa, ma’aikatar lafiya ta ƙasa za ta biya su sama da naira biliyan 4 nan da mako ɗaya bayan cimma yarjejeniyar.
Sanarwar da ma’aikatar lafiyar ta fitar ta ce, gwamnatin za ta biya kuɗaɗen Ariya na likitocin da kuma aiwatar da kwaskarima ga mafi karancin alabashi da aka cimma yarjejeniya a watan Disambar 2019 kuma shugaban Buhari ya sanya hannu.
Matuƙar ba ku yi aiki ba, ba za mu biya ku albashi ba – Gwamnatin tarayya ga ƙungiyar NARD
a cewar sanarwar, tuni gwamnatin tarayya ta aika da sunayen Asibitoci 38, ga ofishin kasafin kuɗi don tantancewa tare da biyan su haƙƙokin su.
Kungiyar likitocin ta tsunduma yajin aikin sai baba ta gani a ranar 2 ga watan Agusta, sakamakon ƙin cika alƙawuran da ta zargi gwamnatin tarayya da yi akan matsayar da suka cimma a baya.
You must be logged in to post a comment Login