Labarai
Yajin aiki : An tashi baram-baram a tattaunawa da kungiyar kwadago da gwamnati
An tashi baram-baram bayan da aka kwashe awa 8 ana tattaunawa da gwamnatin tarayya da kungiyar kwadago ta kasa biyo bayan rashin cimma matsaya.
Wannan na dauke cikin sanarwar da mataimakin shugaban kungiyar kwadago ta ta kasa Ameachi Asugwani ya fitar cewa gwamnatin na son cimma kudoruri a taron amma ta kasa samar da mafuta wajen warwae matsalar
Ameachi Asugwani ya ce kungiyar kwadago na bukatar gwamnatin tarraya ta yi nazari kan karin kudin man fetur da wutar lantarki a kasar nan wanda ya sababa ta tashin gwauran zabi na kayayyakin masarufi a kasar nan
Sai dai a cewar gwamnatin taq yi karin ne saboda ta janye tallafin da take baiwa dilalan mai.
A dai ranar Litinin ne kungiyar kadago ta kasa ta baiwa gwamnatin tarayya wa’adin kwanaki 7 ta janye karin firashin man ko kuma ta tsunduma yajin sai baba ta gani.
You must be logged in to post a comment Login