Labarai
Muna kan bakar mu na ƙin biyan albashi ga masu yajin aiki – Buhari
Gwamnatin tarayya ta ce, har yanzu tana kan batun ta na ƙin biyan albashi ga likitocin da ke yajin aiki a fadin kasar nan.
Ministan ƙwadago da samar da aikin yi Cris Ngige ne ya bayyana hakan a zantawar sa da manema labarai na fadar shugaban ƙasa a ƙarshen mako.
Ngige ya ce, a shirye ta ke ta janye ƙarar da ta shigar gaban kotun ɗa’ar ma’aikata kan batun yajin aikin da ƙungiyar likitoci masu neman ƙwarewa ke yi, matuƙar za su dawo bakin aiki.
Gwamnati ba ta biyamu albashin watan Agusta ba – NARD
Tun da fari ƙungiyar NARD ta ƙalubalanci gwamnatin tarayya kan ta janye matakin ta na shigar da ƙara gaban kotun ɗa’ar ma’aikata na tabbatar da dokar babu aiki babu biyan albashi ga ma’aikatan.
Ƙungiyar ta zargi gwamnatin tarayya kan rashin sauraron ƙorafe-ƙorafen su gabanin ɗaukan matakin rashin biyan su albashi.
You must be logged in to post a comment Login