Labaran Kano
‘Yan Arewa su daure su karbi bashin CBN – Masani
Masanin tattalin arziki nan Jami’ar Bayero da ke nan Kano kuma tsohon kwamishinan kudi na jihar nan, ferfesa Isa Dandago ya shawarci ‘yan Arewa da su karbi bashin da babban bankin kasa na CBN ke fara shirin bayarwa don bunkasa harkokin kasuwancin su
Farfesa Isah Dandago ya ce shirin da babban bankin kasa CBN zai fito da shi zai bai wa masu kananan da matsakaitan sana’o’i bashi mara ruwa zai taimaka wajen farfado da tattalin arzikin kasa.
Tsohon Kwamishinan kudin Ferfesa Isa Dandago ya bayyana hakan ne a yau jim kadan bayan kammala shirin ’’Barka Da Hantsi’’ na nan Freedom Radio.
Yana mai cewa, masu gudanar da kasuwanci a kasar nan na tsoron karbar bashin kudi daga banki, sakamakon kudin ruwa da ake sawa sai dai a wannan karon bankin ya bijiro da sabon tsari.
Sai dai ya ce rancen an tsara shi kashi biyu ne, akwai wanda akwai kudin ruwa a ciki da kuma wanda babu kudin ruwa kasancewar da dama al’umma bas u cika mu’amala da rancen kudin ruwa ba.
Ferfesa Isa Dandago ya ce, har yanzu anan Areweaakwai bukatar wayar da kan al’ummar kasar nan wajen ganin sun fahimci shirin.
You must be logged in to post a comment Login