Labarai
Yan Bindiga sun hallaka mutum 7, tare da jikkata wasu 5 a Birnin Gwari

Wasu ƴanbindiga sun kai wani sabon hari a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna a arewacin duk da sulhun da aka yi a yankin.
Ƴanbindigar sun ƙaddamar da harin ne a garin Kuyallo da ke yankin Birnin Gwari jihar Kaduna, wanda ya yi sanadin asarar rayuka.
Mazauna yankin sun ce mutum tara aka kashe a harin, wasu kuma suka tsira da munanan raunuka.
Rundunar ƴansandan jihar Kaduna ta tabbatar da harin amma ta ce mutum bakwai aka kashe, mutum biyar kuma suka ji rauni.
You must be logged in to post a comment Login